Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan  ya bayyana marigayi Umaru Musa Yar’adua, a matsayin jagora mara son zuciya, wanda “samun irinsa sai an tona” a Najeriya.

A wani cigaban kuma tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan Da yake jawabi kan tsohon uban gidan nasa, Jonathan ya bayyana marigayi Umaru Musa Yar’ Adua, a matsayin jagora mara son zuciya, wanda “samun irinsa sai an tona” a Najeriya.

Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana cewa tsohon shugaban na Najeriya jagora
ne mai kishin al’ummarsa, maras son kai.

Shekaru 12 kenan da rasuwar Umaru Musa Yar’ Adua, Dr. Jonathan ya ce samun shugaban kasa irin marigayin yana da matukar wahala. Jonathan ya fitar da wani sakon ta’aziyya na musamman ne da ya yi wa take da ‘Shugaban kasa Yar’Adua: bayan shekara 12’ a shafinsa na Facebook.

Yar’Adua ya rasu ne a rana irin ta yau a shekarar 2010. Marigayin ne ya karbi mulki a hannun Olusegun Obasanjo, amma ya rasu yana ofis.

A karshe Jonathan ya kare sakon ta’aziyyarsa da cewa samun irin Marigayin, yana da wahala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *