Sarkin Bayero ya yi wannan kiran ne a jiya yayin bikin gargajiya na Hawan Nasarawa a gidan gwamnati da ke Kano.
Hawan Nasarawa biki ne na karramawar da sarkin ya yiwa gwamnan jihar bayan kammala bukukuwan Sallah.
Sarkin ya kuma shawarci matasan jihar da su nisanci aikin barna, musamman shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula.
Hakazalika ya roki iyaye da su sanya ido kan motsi da ayyukan ‘ya’yansu domin gujewa duk wata damuwa.
Ya yi tir da barazanar ‘yan daba a jihar tare da yin kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da sa ido.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da zama lafiya da juna ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba.