Jam’iyyar APC mai mulkin kasarnan ta ƙara wa’adin sayar da fom ɗin takararta a dukkannin matakai.

Jam’iyyar APC mai mulkin kasarnan ta ƙara wa’adin sayar da fom ɗin takararta a dukkannin matakai yayinda ‘yan takara ke ƙara tururuwar sayen tikitin takarar shugaban ƙasa.

Tun farko an tsara kammala sayar da fama-faman ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Mayu.

Sai dai, cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa ya fitar ranar Laraba, jam’iyyar ta ƙara wa’adin zuwa ranar Talata, 10 ga Mayu.

A cewar wani sabon jadawali da Sakataren Tsare-Tsare na APC na Ƙasa Sulaiman Muhammad Argungu ya fitar, an saka ranar 11 ga Mayu a matsayin ranar da dukkannin ‘yan takarar zasu miƙa fama-faman da suka cike.

Yanzu za a gudanar da tarukan zaɓar wakilai wato daliget a dukkannin ƙananan hukumomi na Najeriya daga 12 zuwa 14 ga watan na Mayu.

Lamarin na zuwa ne yayinda jam’iyyar ke ci gaba da samun ‘yan takara musamman na shugaban ƙasa, inda a jiya Laraba Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da tsohon shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole suka ƙaddamar da takarar tasu.

Kazalika, Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya ayyana tasa takarar a jam’iyyar APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *