Alhazan da suka kammala aikin Umrah a kasa mai tsarki sun shiga tsaka-mai-wuya bayan da hukumomin kasar Saudi Arabiya suka dakatar da tashin jirage.

Alhazan da suka kammala aikin Umrah a kasa mai tsarki sun shiga tsaka-mai- wuya bayan da hukumomin kasar Saudi Arabiya suka dakatar da tashin jirage daga wani bangare na filin jiragen saman na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah tsawon sa’a 48.

Alhazan daga kasashe da dama, ciki har da Najeriya, sun tsinci kansu cikin wannan hali ne saboda cinkoson da aka samu a bangaren tashin matafiya na filin jirgin, saboda abin da suka kira fitowar matafiya fiye da sa’a 12 gabanin tashinsu.

Lamarin dai ya shafi wasu kasashen Afrika, ciki har da Najeriya, abin da ya sa wasunsu suka koka saboda yawancinsu duk guzuri ya kare.

Alhaji Abubakar, ya je Umrah ne daga jihar Kano a Najeriya, kuma yana daga cikin wadanda wannan mataki ya shafa, ya shaida cewar bayan sun kammala Umrarsu, yanzu fitowa daga kasa mai tsarki ita ce matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *