A yau ne tsohon Shugaban Kasa, Umaru Musa Yar’Adua ke cika shekara 12 da rasuwa.

Marigayi Umaru Musa Yar’Adua,  ya rasu ne a shekarar 2010 sakamakon rashin lafiya, shekara uku bayan zamansa shugaban kasa a shekarar 2007.

Gwamnatin Umaru Musa Yar’Adua ta yi fice da Manufofi Bakwai da ta gabatar, da kuma yadda shi kansa ya amince da cewa zaben 2007 mai cike da rudani da ya kawo shi kan kujera na cike da kura-kurai, ya kuma daura damarar gyarawa.

Bangarorin da gwamnatinsa ta ba wa fifiko su ne na wutar lantarki, makamashi da ababen more rayuwa; wadata kasa da abinci; samar da arziki; sufuri; tsaro; ilimi; samar da ayyuka; sai kuma gyara dokokin kasa da filaye.

Marigayin wanda aka haifa a ranar 6 ga watan Agusta, 1951, ya kasance Gwamnan Jihar Katsina daga 1999 zuwa 2003, inda ya gudanar a muhimman ayyuka da ake ganin har yanzu gwamnatocin da suka biyo baya ba su kama
kafarsa ba.

A lokacin da yake gwamanan Katsina, ya kasance gwamnan farko da ya bayyana kadarorinsa a bainar jama’a sannan ya kawo muhimman ayyukan ci gaba.

Shi ne gwamna na biyar a Arewacin Najeriya da ya fara dabbaka shari’ar Musulunci, ya gina makarantu, kuma ana ganin ya cika alkawarinsa na gudanar da gwamnati cikin gaskiya da rashin almundahana.

Bayan rasuwarsa ne mataimakinsa, Goodluck Jonathan ya zama shugaban kasa, ya karashe wa’adinsa zuwa shekarar 2011, daga bisani ya yi nasa wa’adin dayazuwa 2015, inda aka kayar da shi a lokacin da yake neman tazarce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *