Tsohon shugaban kasar ya nuna duk halin da aka shiga da cewa abu ne mai wucewa kuma bada dadewa ba za a samu mafita a nan Najeriya.
Olusegun Obasanjo ya yi wannan jawabi a wajen wani taron addu’a da mabiya wata coci suka shirya a birnin Aboekuta, da ke jihar Ogun.
Obasanjo ya yi kira ga al’ummar Najeriya su yarda da Ubangiji, su sa ran abubuwa za su canza zani, ya ce ba za a cire tsammanin rahamar Allah ba.
Lura da yadda abubuwa su ke tafiya yau a kasar nan da ma fadin Duniya, tsohon shugaban ya ce ya zama wajibi Bayin Allah su komawa Mahallicinsu.