“Mulki zai koma Kudu ne kawai idan aka zabo ‘yan takaran manyan jam’iyyun siyasa biyu daga Kudu”. – Sanata Shehu Sani

A wani sako da Sanata Shehu Sani ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 3 ga watan Mayu, Ya ce yiwuwar shugabancin kasar nan ya koma kudu ya ta’allaka ne da shawarin manyan jam’iyyu biyu (APC da PDP) su fito da ‘yan takara daga yankin. Sani, tsohon dan majalisar tarayya kuma jigo a jam’iyyar PDP daga jihar Kaduna.

Idan za ku iya tunawa, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na PDP kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce dole ne a ba dan yankin kudu maso gabashin kasar nan mulkinta,

Ya tsaya akan cewa zaben shugaban kasa dan kabilar Ibo ne kadai adalci da kuma nuna girma ga yankin don haka wajibi ne a ba su dama, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Obi ya yi wannan maganar ne a ranar Litinin yayin wani taro da wakilan jam’iyyar na Jihar Ogun da sauran shugabannin jam’iyyar PDP a ofishinta da ke Abeokuta, Jihar Ogun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *