Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce an fara bincike kan gobarar da ta tashi a ofishinta da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.


Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Litinin, ba tare da samun asarar rai ba, yayin da muhimman kayan aiki na katunan zabe da na’urar rajistar masu kada kuri’a basu sami matsalar komai ba.

Sai dai hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara da wasu matasa sun yi kokarin
shawo kan gobarar.

A cewar Okoye Tuni ‘yan sanda da hukumar kashe gobarar jihar suka fara bincike don gano musabbabin tashin gobarar don bai wa INEC shawara kan daukar matakin da ya dace.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da
kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya
fitar a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *