Matashin ya wallafa haka ne ta shafinsa na Twitter. Ya ce lokaci ya yi da ’yan Najeriya za su san gaskiyar lamarin da ya kai ga rasuwar mahaifinsa, ya kuma ce kamata ya yi shugaban kasa ya duba rumbun adana bayanai.
A cewarsa zai taimaka wa shugaban kasar wajen tona asirin mutuwar marigayi MKO Abiola, inda jaddada cewa irin wannan mataki ne kawai zai tabbatar da adalci.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa Abiola ne ake kyautata zaton ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, amma shugaban kasa na wancan lokacin, Janar Ibrahim Babangida ya soke zaben.
Amma Abiola ya bayyana kansa a matsayin shugaban kasa a wani abin da ake kira Epetedo, abin da ya sa daga bisani gwamnatin soja ta marigayi Janar Sani Abacha ta daure shi.
Shugaba Buhari ya karrama Abiola da lambar girmamawa ta GCFR, wadda shugabannin Najeriya ne kadai suka kebanta da ita.
Buhari ya kuma ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuradiyya maimakon ranar 29 ga watan Mayu da ake bikin a baya.