An ceto fasinjoji 50 yayin da tayar jirgin DanaAir da ke kan hanyarsa zuwa Legas daga fatakwal ya kama wuta.

Akalla fasinjoji 50 ne da ke cikin jirgin DanaAir da ke kan hanyarsa ta zuwa Legas aka ceto bayan tayar da ya yi wuta kafin ya tashi a filin jirgi na Fatakwal.

Da yake magana akan lamarin, wanda ya faru a ranar Litinin, Kakakin Dana Air, Kingsley Ezenwa, a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce ba a rasa rai ko fasinja da ya jikkata.

Mista Ezenwa ya bayyana cewa jirgin mai lamba 5N JOY ya tashi daga Fatakwal zuwa Legas lokacin da lamarin ya faru.

Sanarwar ta ce, “Jirgin mu mai lamba 5N JOY daga Fatakwal zuwa Legas a ranar 2 ga watan Mayu 2022 ya shirya tashi lokacin da matukin jirgin ya lura da wata matsala.

Ya kuma ce: Muna matukar ba dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin hakuri bisa abin da ya faru sakamakon soke jirgin.

“A Dana Air, lafiyar fasinjojinmu da ma’aikatan jirgin su ne babban fifiko a duk fannonin ayyukanmu kuma za mu ci gaba da aiki bisa ka’idojin zirga-zirgar jiragen sama da mafi kyawun ayyuka na duniya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.