Kwanan nan za’a yi wa shugaban kasar rasha aikin tiyata cutar daji, ana sa ran zai mika mulki ga wani tsohon dan leken asirin KGB.

Kwanan nan za’a yi wa Vladmir Putin aikin tiyatar cutar daji kuma ana shirin mika mulki ga tsohon shugaban KGB. Hardliner Nikolai Patrushev zai jagoranci yakin Ukraine har Putin ya samu lafiya, in ji rahotanni.

Janar SVR ya ruwaito cewa Putin ya kamu da ciwon daji na ciki da kuma cutar Parkinsons a watanni 18 da suka gabata.

Wannan labarin ya zo ne a daidai lokacin da ake sa ran Putin zai kaddamar da farmaki a duk fadin kasar ta Ukraine tare da ba da umarnin tattara dimbin mazaje masu shekarun soji don shiga sojan.


An shirya aikin tiyatar a rabin na biyu na Afrilu amma an jinkirta, in ji SVR. “An shawarci Putin da a yi masa aikin tiyata amma har yanzu ana kan tattauna ranar da za’a yi yanzu” in ji sanarwar.

Janar SVR ya kuma cewa: ‘Da alama babu wani gaggawa na musamman, amma kuma ba za a iya jinkirta shi ba.’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *