Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta (EFCC), tana neman wasu mutune su 59 bisa zargin damfarar wasu kudade masu yawa da suka kai naira biliyan 435 da wasu dala $397,758,000.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta (EFCC), ta ayyana neman wasu mutune su 59 ruwa a jallo, bisa zargin badakala da damfarar wasu kudade masu yawa da suka kai naira biliyan 435 da wasu dala $397,758,000.

Daga cikin mutum 59 hudu daga ciki jami’an gwamnatin jihar Ribas ne, ciki kuwa har da babban Akanta na jihar, Fubara Siminayi, da ake nema bisa zargin badakalar kudade har naira biliyan N117, ana kuma zarginsa da almubazzaranci da dukiyar jama’a, fitar da kudade ba bisa ka’ida ba da kuma zubar da kimar ofishinsa.

Hukumar wacce ta wallafa jerin wadanda take neman bisa zarge-zargen da suka hada da hada-hadar kudade ta hanyar damfara, laifukan da suka shafi amfani da internet, fitar da takardar cekin kudi ta haramtacciyar hanya da sauransu. 

Shugaban sashen yada labarai na EFCC, Wilson Uwujaren, ya bukaci jama’a da su taimaka musu da bayanan gano inda wadanda ake neman suke da sanar da hukumar ko ofishin jami’an tsaro mafi kusa da su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *