An yi rashin rayukan mutane 4 yayin da wasu 20 suka samu raunika masu firgitarwa a rushewar wani bene mai hawa uku a ebute meta da ke jihar legas.

Wata mata mai sana’ar sayar da burodi da danta da kuma karin wasu mutum biyu sun mutu bayan wani bene mai hawa uku ya rushe a unguwar Ebute-Metta da ke Jihar Legas ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce an kuma samu nasarar ceto mutum 23 daga cikin baraguzan ginin.

Benen dai wanda ke kan titin Ibadan Street ya rushe ne wajen misalin karfe 9:30 na daren Lahadin, kuma ana zargin har yanzu akwai ragowar mutane a cikin shi.

Tuni dai jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas da na takwararta ta ba da Agajin Gaggawa (LASEMA) suka dukufa aikin ceto a wajen.

Wata majiya ta ce ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, an ceto akalla mutum 23.

An yi rashin rayukan mutane 4 yayin da wasu 20 suka samu raunika masu firgitarwa a rushewar wani bene mai hawa uku a ebute meta da ke jihar legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *