Wasu Musulmai sun saba Umarnin Sarkin Musulmi, sun gudanar da Sallar idi a Sokoto.

Wasu Musulmai a jihar Sokoto sun gudanar da Sallar Idi yau Lahadi wanda ya saɓa wa umarnin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, wanda ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Eid-ul-Fitr. Daily trust ta rahoto cewa a ranar Asabar, Sarkin Musulmai ya sanar da cewa ba’a ga jinjirin watan Shawwa 1443AH ba a sassan Najeriya.

Mafi yawan Musulman, waɗan da mabiya ne ga Sheikh Musa Lukwa, sun gudanar da Sallar idi wato ƙaramar Sallah da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi.

Da yake zantawa da wakilim jaridar, Sheikh Lukwa, ya ce sun samu sahihan bayanan ganin jinjirin watan Shawwal a wasu sassan Najeriya da wasu ƙasashen waje.

A jawabinsa, yace Musulmai sun ga wata jihohi biyar na Jamhuriyar Nijar, inda ya ƙara da cewa: “Na kalli bidiyon shugaban ƙasar su (Nijar) lokacin da yake ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar idin ƙaramr Sallah, kuma an ga wata a ƙasar Afghanistan, Mali da wasu ƙasahen Afirka kuma sun gudanar da Sallah yau.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *