SIYASA 2023: Oshiomhole Ya Yi watsi da burin sa na neman kujera Majalisar Dattawa, zai ayyana aniyarsa tsayawa takarar shugaban kasa kai tsaye a talabijin.

A Yau Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ya yi watsi da burinsa na neman kujerar majalisar dattawa.

Sai dai Oshiomhole, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce yau zai ayyana aniyarsa tsayawa takarar shugaban kasa a talabijin kai tsaye.

Sanarwar tace, “Gayyata ta Musamman: “Ina gayatan ku na musamman zuwa ga sanarwar da Kwamared Adams Oshiomhole ya yi na tsayawa takarar shugaban kasa a Tarayyar Najeriya a zaben 2023, karkashin jam’iyyar APC.” An bayyana karara cewa za a gudanar da sanarwar a yau (Juma’a) 29 ga Afrilu, 2022 a Cyprian Ekwensi Center for Arts and Culture, Area 10 Abuja.

Za a fara ayyana tsohon gwamnan jihar Edo a hukumance da karfe 3 na rana.

Idan dai za a iya tunawa, Oshiomhole a makonnin da suka gabata a yayin bikin cikarsa shekaru 70 da haihuwa a gidan sa, Iyamoh ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa.

Oshiomhole ya bayyana cewa zai tsaya takarar Sanatan Edo ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a 2023. A halin yanzu kujerar dai tana hannun Sanata Francis Alimikhena. Jigon na APC, ya bayyana aniyarsa ta karbar mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa’adinsa a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *