Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Rasha data bada hadin kai ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Rasha data bada hadin kai ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, a binciken da zata gudanar kan zargin aikata laifukan yaki a Ukraine.

Guterres na jawabi ne a Bucha, inda ake zargin dakarun Rasha da kisan daruruwan fararen hula.
Ya ce ya na goyon bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya kan wannan batu, kuma yana kira ga Rasha data baiwa kotun hadin kai.

Ya kuma ziyarci garuruwa da dama a arewa maso yammacin Kyiv, inda Rasha ta yi luguden wuta.
Dama shugaban ya isa Kyiv domin ganawa da shugaba Volodomyr Zalensky, kwanaki biyu bayan ganawa da shugaba Putin

Leave a Reply

Your email address will not be published.