Jam’iyyar APC ta dauke aikin sayar da fom din takara na zaben 2023 zuwa Babbar Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa (ICC) da ke Abuja.

Jam’iyyar ta dauke sayar da fom din takarar ne daga sakatariyarta ta Kasa, washe garin da wasu da ba’asan kosu wanene ba suka sace tsabar kudi Dala dubu hamsin a wurin sayar da fom din.

Da yake sanar da sauya wurin sayar da fom din, Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Kasa, Barista Felix Morka, yace anyi hakan ne domin saukaka zirga-zirgar jama’a da ababen hawa, ganin yadda cincirindon jama’a ya haifar da cunkoso a kusa da sakatariyar jam’iyyar.

Felix Morka, ya kuma bayyana cewar Dala dubu hamsin din da aka sace mallakin wani mutum ne, bana jam’iyyar ba.
Tun bayan da jam’iyyar ta fara sayar da fom din takara na zaben takara na 2023 ne dai masu son tsayawa takara suka yiwa wurin tsinke domin sayen fom.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *