Mai Jama’a Abdullahi, kakakin rundunar NDLEA ta Kaduna,ne ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai.
A cewar Abdullahi, kwayoyin sun kai nauyin tan1.2 sannan an kama maganin tari na codeine yayinda jami’an hukumar suka kai wani samame a ranar Litinin da Talata.
Kakakin rundunar ya cigaba da bayyana yadda aka kwace kwayoyin tramadol din a karamar hukumar Zaria a ranar Litinin, yayinda aka kama wanda ake zargin a wata gonar kaji dake jihar.
Haka zalika, ya ce ana cigaba da bincike don gano wanda akayi kokarin kaiwa sakon a Kaduna.
Abdullahi yace a cikin watan Afirilu an kama mutane 73 a fadin jihar, wadanda ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi.