Al’ummar garin Goya da ke karamar hukumar Funtua a jihar Katsina sun tsinci kansu cikin wani yanayi na fargaba sakamakon artabun da suka yi da jami’an tsaro a makon da muke ciki.

Rahotanni sunce al’amarin ya faru ne bayan samamen da ‘yan sanda suka kai musu tare da yin harbe-harben kan mai-uwa-da-wabi.

Yayin samamen, mutanen garin sun zargi ‘yan sanda da yin harbin da ya yi sanadin kashe mutum ɗaya da raunata wasu tare da farfasa ababen hawa.

Sai dai ‘yan sanda sun ce mutanen garin ne suka fara auka musu da sara da jifa al’amari da ya janyo mutuwar jami’insu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *