‘Yan sanda sun kama tsohon shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, a Abuja. Rimingado dai an kama shi ne a masaukin Gwamnan Sokoto da ke Abuja, inda ya je tantance shi a matsayin dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kama shi tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa a wata tattaunawa ta wayar tarho a Kano.
Yace: “Eh gaskiya ne an kama Muhuyi a masaukin Gwamnan Sokoto da ke Abuja,”
An tattaro cewa ‘yan sandan sun tafi da shi kai tsaye bayan an tantance shi inda suka kai shi babban birnin tarayya.
A ranar 28 ga Maris, 2022, ‘yan sanda sun kewaye gidan Rimingado da ke Kano amma suka kasa kama shi.