Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa duk kasashen da suka shigarwa Ukraine faɗa a yaƙin da take yi da ita za su gamu da abin da ya kira martani cikin sauri kamar ƙiftawar walƙiya.

Da yake magana da ‘yan majalisar kasar a birnin Moscow, ya ce Rasha na da manyan matakan da za ta iya dauka idan hakan ta kama.

Rasha ta kakaba wa ‘yan majalisar dokokin Burtaniya sama da 200 takunkumi da kuma tsoffin ‘yan majalisar.

A halin da ake ciki kuma, Rasha ta dakatar da samar da iskar gas zuwa kasashen Bulgaria da Poland a yau ta hanyar bututun Yamal da Europa.

Wannan ramuwar gayya dai shi ne mafi muni a cikin wadanda suka yi a baya, kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Europa suka bi sahun Amurka wajen kara kai kayan yaki domin taimakawa Ukraine din dakile wani sabon harin da Rasha ta kai a gabashin kasar.

Rage iskar gas din ba zai sa kasashen cikin matsala ba saboda su ma sun yi nasara wajen samun, iskar gas ta wasu hanyoyin tun shekaru 7 da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *