Rundunar sojin Najeriya ta fitar da wasu hotunan da ke nuna yadda ta lalata mafakar ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP a yankin Kasha Kasha ta jihar Borno a yau Talata, 26 ga watan Afrilu. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rundunar ke kara kaimi wajen dakile munanan ayyukan ‘yan ta’adda a Arewancin Najeriya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da rundunar ke kara kaimi wajen dakile munanan ayyukan ‘yan ta’adda a Arewancin Najeriya. Rundunar ta ce, dakarun bataliya ta 195 tare da mambobin CTJTd ne suka yi wannan aiki a wani samamen da suka kai kan ‘yan ta’addan.
Hotunan na shafin rundunar sojin na Twitter sun nuna alamar gawargwakin ‘yan ta’addan da kuma kayayyakin da aka lalata. Hakazalika, sanarwar d ake tattare da hotunan ta bayyana cewa, an kwato kayayyakin barna daga hannun ‘yan ta’addan.