Hukumomi a birnin Shanghai na China, sun yi amfani da korayen karafa wajen katange kofofin gidajen mutane a na shaguna a tituna akamakon karuwar masu cutar korona a birnin.
Mazauna unguwannin sun wayi gari da ganin korayen karafan da aka shinge gidajensu da shi ba tare da an sanar da su ba.
Wani mazaunin Shanghai ya shaidawa BBC cewa, ya wayi garin ranar Talata da ganin koren karfen tokare a kofar gidansa babu kuma wanda ya yi masa bayanin komai.
Makwannin da suka gabata dai rabin birnin Shanghai mai al’umma miliyan 25 ya kasance karkashin dokar kulle, saboda sake barkewar cutar korona.
An wallafa hotunan jami’ai sanye da tufafin kariya, su na rufe kofafon gidaje da kantuna, d mkarantu da wuraren taruwar jama’a.
Yawancin karafan sun kai tsahon mita biyu, kuma yankin da aka sanya karafan mutum daya ne kadai gwaji ya nuna ya na dauke da cutar korona.