Hukumar tabbatar da inganci kayayyaki a Najeria wato (SON) ta bayyana damuwa kan ƙaruwar shiga da kayayyaki marasa inganci a cikin ƙasar

Hukumar tabbatar da inganci kayayyaki a Najeria wato (SON) ta bayyana damuwa kan ƙaruwar shiga da kayayyaki marasa inganci a cikin ƙasar musamman na abinci.

Shugaban Hukumar Malam Farouk Ali Salim, ya shaida wa BBC cewa, wannan matsalace babba saboda a yanzu duk kasuwar da akaje a Najeriya, idan ka dauki kaya kashi 8 a
cikin 10 duk suna da matsala.

Ya ce ko ta wajen tantance kayan ko kuma lokacin amfaninsu ya kare, wanda hakan kuma zai iya sa tattalin arzikin kasar ya gamu da cikas matuƙar gwamnati ba ta
ɗauki matakin daƙile matsalar ba.

Ana dai fama da matsalar shigarwa da kuma sayar da kayayyaki marassa inganci a kasuwannin Najeriya, in da a wasu lokuta sai ka sayi abu amma da zarar ka duba lokacin lalacewarsa sai kaga ya kusa koma ya cika wa’adin.

Masharhanta na ganin wannan kuwa na da nasaba da laifin masu shigo da kayayyaki cikin kasar wadanda basa kiyaye da dokoki da ma ka’idoin shigo da kaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *