Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta samu nasarar kame Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wani attajirin da ake zargin yana da hannu a harkallar safarar miyagun kwayoyi ta DCP Abba Kyari da tawagarsa.
Sanarwar da NDLEA ta fitar ta bayyana cewa Afam na da hannu dumu-dumu a harkallar shigo da miyagun kwayoyi na Naira biliyan 3 da ke da alaka da Abba Kyari.
Bayan shafe watanni ana sa ido akansa, an kama Mista Ukatu wanda shi ne shugaban Kamfanin Mallinson Group of Companies, a cikin jirgin da zai je Abuja daga filin jirgin saman Legas, Ikeja a ranar Laraba 13 ga Afrilu.
Hukumar ta ce Afam babban mai shigo da miyagun haramtattun kayayyaki ne, wadanda suka hada da kwayoyin Tramadol da dai sauransu.