Kungiyar Dattawan jihar Katsina, ta yi kira ga Minista Raji Babatunde Fashola ya duba batun aikin titin Kano-Katsina

Kungiyar Dattawan jihar Katsina, ta roki Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola ya duba batun aikin titin Kano-Katsina. A wani rahoto da aka fitar a yau Litinin, 25 ga watan Afrilu 2022, an ji kungiyar dattawan ta jihar katsina ta kai rokonta gaban Raji Babatunde Fashola.

Manyan na jihar Katsina su na so Ministan ya umarci ‘yankwangila su koma kan aiki a wannan titin da yanzu aka yi sama da watanni uku da daina aikinta.

Sakataren kungiyar, Alhaji Aliyu Sani Mohammed ya bayyana hakan yayi hira da manema labarai a garin Katsina.

A cewar sakataren kungiyar, ba su san gaskiyar dalilin tsaida wannan aiki ba, amma ana rade-radin kamfanin CCECC su na so a sallami na kan hanyar ne.

Inda suka bayyana cewa Akwai mutanen da za a bawa kudi, a tada da su daga kan titin. Wanda muddin gwamnatin tarayya ba ta sallame su ba, ba zai yiwu a cigaba da aikin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *