Kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta ɗauki alhakin kashe ‘yan sandan Najeriya a Jihar Kogi

Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kashe ‘yan sandan Najeriya a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan ofishinsu a Jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar ranar Asabar.

Kungiyar ta ce mayaƙanta sun buɗe wa ofishin wuta da mashinga tare da kashe ‘yan sanda biyar a Ƙaramar Hukumar Adavi, sun bayyana haka a wata sanarwan da ta fitar a dandalin sadarwa na Telegram

Sai dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce dakarunta uku aka kashe.

Ba a saba ganin ‘yan ƙungiyar sun kai hari yankin ba, tana mai cewa ta kai shi ne saboda ɗaukar fansar kashe kwamandojinta da jami’an tsaron Najeriya ke yi a kwanan nan.

Kazalika, ƙungiyar ta ce ita ce ta kai hari kan wata mashaya a Jihar Taraba kwana ɗaya kafin wannan harin na Kogi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *