Birnin Shanghai na kasar China mai hada-hada ya rawaito cewar an samu mutum 39 da suka mutu sakamakon annobar korona a ranar Asabar – adadi mafi yawa da ake samu tun tsaurara dokar
kulle makonni hudu da suka gabata.
A ranar Litinin da ta gabata aka bada rahoton mutum na farko da ya mutu tun sake dawowar annobar, da kuma samun dubbai da suka kamu a rana guda.
Birnin Shanghai mai al’umma miliyan 25 yanzu haka na fama da barkewar wannan annoba mafi girma a China kawo yanzu.
Ana cigaba da daukar matakai masu tsauri, da kwashe mutane daga gidajensu domin yi feshi. Sannan a Beijing, jami’ai na gargadi kan barazanar da cutar da ke yaduwa cikin gaggawa ke haifarwa.