Aisha Buhari ta yi kira ga masu neman takarar shugaban kasa da su dauki mata a matsayin abokan takara

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bukaci jam’iyyun siyasar Najeriya da su yi la’akari da daukar mata a matsayin abokan takara ga ‘yan takarar da ke neman mukamai daban-daban a fadin kasar nan a zaben 2023.

Aisha ta yi wannan kiran ne a daren ranar Asabar a lokacin da ta karbi bakuncin masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyun siyasa daban-daban a wani buda-baki na Ramadan a fadar gwamnati da ke Abuja.

Uwargidar shugaban kasar ta shirya taron buda bakin ne domin ba masu neman takarar damar wanzar da soyayya da farin ciki a tsakaninsu a cikin wannan wata ta Ramada da kuma kokarin hada kan kasa.

Ta ce: “A zahirin gaskiya, lokaci ya yi da za a tsayar da mata a matsayin abokan takara a dukkan matakai duba ga karfin kuri’unsu da kuma yadda suke taka rawa a tsare-tsaren siyasa. “Yayin da muke tunkarar zaben 2023 da kyakkyawan fata, ina da yakinin cewa Najeriya za ta ci gaba da habbaka daga karfi zuwa karfi a kan turbar dimokuradiyyarmu.”

An ruwaito cewa, daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar da suka halarta a yayin rubuta wannan rahoton, akwai jigon jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da gwamnan Bauchi, Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published.