SIYASA 2023: Dan Takarar Shugaban Kasa Adamu Garba yayi kira ga ‘yan Najeriya da su taimaka da gudummawar kudi domin ya samu siyan fom ɗin takara na apc.

Wannan labari na zuwa ne bayan da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Felix Morka, a ranar Laraba ya bayyana cewa fam din tsayawa takara zai kai naira miliyan 70, yayin da fam miliyan 30 na neman takara.

Garba, wanda ta shafinsa na Twitter ya bayyana kaduwarsa dangane da wannan sanarwar, a yanzu haka yana neman taimakon ‘yan Najeriya domin bayar da gudumawa, domin ya sayi fom din.

A cewar Garba, gudumawar hadin gwiwa domin samun fom din zai aike da sakon cewa ‘yan Najeriya musamman matasa sun damu da kasa.

Ya kuma buga bayanan asusun nasa, yayin da ya bukaci masu bayar da gudummawar da su tabbatar sun kara lambobin wayar su.

Yace; “Yan Nijeriya,

“Aiki na da ku ya fara. Ga wadanda suka yi alkawarin bayar da gudummawa, ga lambar asusun

“1008404148 | Zenith

“Bai kamata a siyar da fom miliyan 100 ba, amma gudummawar da zamu bayar don samun wannan fom za ta nuna cewa mun damu da Najeriya.

“Muna ba da shawarar ku haɗa lambobin wayarku a cikin sashin labari idan zaku turo da kudi ko kuma, kuna iya kiran lambobin waya masu zuwa:

“Na gode.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *