Gidaje 463 ne sun lalace, mutune sama da 1,300 sun rasa muhallansu sakamakon ruwan sama mai karfi a 2022.

Akalla gidaje 463 ne suka lalace baya ga mutune sama da 1,300 da suka rasa muhallansu sakamakon ruwan sama mai karfi da aka samu a farkon daminar wannan shekarar.

Wuraren da aka samu wannan iftila’i su hadarda yankunan kananan hukumomin Obudu da Yala da kuma Ogoja na Jihar Ribas, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN
ya ruwaito.

Jami’in Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) a shiyyar, Godwin Tepikor, yace a yankin Karamar Hukumar Obudu kadai, mutune 503 ne lamarin ya shafa tare da lalata gine-gine 249 da kuma dukiyar jama’a.

Jami’in NEMA ya ce, “Iftila’in ya afuku ne a yankin a ranar 5 ga watan Afrilun 2022, inda ya shafi mutune 486 tare da lalata gidaje 214 hade da dukiyoyi.

Tepikor ya ce iftila’in ya auku a yankin Ogoja a ranar ya taba kauyuka da suka hadarda Ishibori da Ukelle da Ogboje da kuma Abakpa, inda ya shafi mutum 337 da gidaje da sauran
kadarorin jama’a.

Jami’in ya ce a dunkule, iftila’in ya shafi mutum 1,326 sannan ya lalata gidaje 463. Hakan na zuwa ne duk da cewar yanzu daminar bana ta fara kankama, lamarin da yasa ake zullumin yadda lamarin zai kasance idan aka shiga tsakiyar damina lokacin da akafi samun ruwan sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published.