An tabbatar da mutuwar mutumn daya yayinda gidaje da shaguna suka kone a jihar Legas.

Akalla mutum daya ne aka tabbatar da mutuwarsa yayinda gidaje da shaguna suka kone bayan da wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a Ajegunle zuwa Alagbado, daura da babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta da sanyin safiyar wannan rana.

Hukumar kashe gobara ta jihar Legas a halin yanzu tana kan yakar gobarar da ta barke a Titin Toll Gate Bus Stop, babban titin Abeokuta, mai iyaka da jihohin Legas da ogun.

An rawaito cewar gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2 na vdare yayinda wasu bata gari ke diban mai daga tankar da ta fadi Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, MargretAdeseye, a lokacin da take karin haske ta ce an gano mutum ndaya da ya mutu a gobarar da kuma motoci uku da suka kone.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *