Gwamnatin tarayya zata tura sojoji 173 kasar Guinea Bissau.

Gwamnatin tarayya zata tura sojoji 173 kasar Guinea Bissau domin gudanar da ayyukan samar da zaman lafiyar a kasar dake fama da rikice rikice.


Babban kwamandan dake kula da ayyuka na musamman a rundunar sojin kasar, Manjo Janar
Oluwafemi Akinjobi ya sanar da shirin lokacin da yake yiwa sojojin jawabi a inda suke samun horo a
Jaji.

Janar Akinjobi yace tun bayan yancin kan Najeriya, kasar ta bada gagarumar gudumawa wajen gudanar
da ayyukan samar da zaman lafiya daya kunshi sojojin ta sama da dubu 100 a kasashe sama da 40
na duniya.

Rahotannin na cewar kwamandan sojojin kasar sun taimaka matuka wajen tabbatar da zaman lafiya a
kasashe daban daban a ciki da wajen Afirka, kuma wannan ya taimaka wajen daga darajar su a idanun
duniya da kuma samun lambobin girma daban daban.

Janar Akinjobi ya gargadi sojojin dasu kaucewa nuna halin rashin da’a a kasar da zasu tafi saboda kare
kima da martabar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *