Wani Direban Bas Ya Kashe Jami’in LASTMA a hanyar Lekki-Ajah, Jihar Legas

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas ta ce wani jami’in su ya gamu da ajalinsa lokacin da yake kokarin kama wani direban mota da ake zargin ya saba dokar titi. An ce jami’in ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Lekki-Ajah da yake Jihar Legas.
“Direban wata koren motar Toyota Sienna, mai dauke da lamba, FST 901 AR, ta afkawa wani jami’in LASTMA, Jamiu O. Issa, wanda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa, a safiyar ranar 19 ga watan Afrilu, 2022,” in ji wata sanarwa da mai magana da yawun LASTMA, Filade Olumide, ya sanyawa hannu ranar Laraba.

“An ce marigayi Issa ya tunkari direban motar Sienna wanda ke tuki a kan hanyar da ababen hawa (Hanya Daya) ke fuskantar motocin da ke tahowa daga Chevron zuwa Titin Conservation Toll Plaza.
A cewar wasu shaidun gani da ido, direban Sienna ya kuma kakkabo wani mutum yayin da yake kokarin tserewa daga wurin kafin a kama direban.

“A daidai lokacin da abubuwan nan ke faruwa, an garzaya da Issa da ya ji rauni zuwa babban asibitin Legas Island inda aka tabbatar da cewa gawarsa aka kawo. An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawarwaki na wannan asibiti.”
LASTMA ta ce babban manajan ta, Bolaji Oreagba, ya ji takaicin faruwar lamarin.

“Ya kuma ce duk da kiraye-kirayen da aka yi da kuma gargadi ga jama’a da su guji cin zarafi da raunata jami’an gwamnati, wasu marasa kishin al’umma da suka ki duk wata bukata za su fuskanci fushin doka.” Sanarwar ta kara da cewa.

“Oreagba ya kuma lura cewa, wannan lamari ba zai sa jami’an hukumar su karaya ba wajen ci gaba da gudanar da ayyuka da ayyukansu kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanada.
“Saboda haka, ya yi kira ga jama’a da su bi dokokin da suka shafi jihar domin kada a saba wa doka da sakamakonta.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *