“Kowa ya bar wayar sa gida” – inji Aisha Buhari yayin yadda za ta shirya liyafa ga ‘yan takarar shugaban kasa a dukkan jam’iyyu.

Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta gayyaci masu neman shugaban kasa zuwa liyafar buda baki a fadar shugaban kasa a ranar Asabar.

Gayyatar wadda aka yi wa dukkan masu fatan zama shugaban kasa a fadin jam’iyyun siyasa, ana sa ran samun mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da wasu ‘yan takara goma sha bakwai daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP ciki har da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike; Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da wasu daga cikin jam’iyyar APC mai mulki ne suka halarci bikin.

Katin gayyata na taron da ya gudana a ranar Alhamis, ya shawarci wadanda suka halarci taron da kada su zo da wayoyin hannun su, inda ya bayyana cewa katin gayyata zai zama takardar izinin shiga.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ofishin uwargidan shugaban kasa, Aliyu Abdullah, ya yi karin haske kan cewa ka’ida ce ga bakin da ke halartar taron a fadar shugaban kasa, da a nemi kada a shiga da wayoyi.

One Reply to ““Kowa ya bar wayar sa gida” – inji Aisha Buhari yayin yadda za ta shirya liyafa ga ‘yan takarar shugaban kasa a dukkan jam’iyyu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *