2023: Mataimakin gwamnan Katsina yayi murabus daga mukamin kwamishinan noma

Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Mannir Yakubu, ya yi murabus daga mukaminsa na kwamishinan noma da albarkatun kasa.

Babban sakataren yada labaran sa, Ibrahim Kallah, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Katsina ranar Alhamis.

Kallah ya ce murabus din Mannir ya yi daidai da sashe na 84 (12) na dokar zaben 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

Ya ce, “Mannir ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 14 ga Afrilu, 2022, a shirye-shiryen sa na ayyana takarar gwamna nan ba da dadewa ba.”

Babban Sakataren Yada Labarai ya kara da cewa Mataimakin Gwamnan ya godewa Allah Madaukakin Sarki da Gwamna Aminu Masari da ya ba shi damar bayar da gudunmuwar “domin dawo da aikin gona a gwamnatin Masari.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Mannir Yakubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka sake fasalin harkar noma inda manoman suka samu sauyi wajen noman noma wanda ya tabbatar da samar da abinci, da bukatun masana’antun noma na jihar da ma Nijeriya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *