Yakin Ukraine: An Saki Daliban Najeriya 13 Daga Gidan Yari a Kasar Poland

Akalla ‘yan Najeriya 13 cikin 19 da ake tsare da su a sansanoni daban-daban a kasar Poland an sako su.
Rahma media ta rahoto cewa sakin nasu ya biyo bayan shigar da jakadan Najeriya a kasar Poland Manjo Janar Christian Ugwu (rtd) ya yi.

Wata sanarwa da Abdur-Rahman Balogun, shugaban sashen yada labarai, hulda da jama’a da kuma ladabi na hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ya fitar a ranar Laraba, ta ruwaito Ugwu na cewa a cikin sauran mutane shida da suka rage a sansanonin da ake tsare da su, daya ya yi ikirarin cewa dan kasar Kamaru ne.

Abin takaici; saura biyar din, duk sun nemi mafaka (makafi) a kasar Poland ciki har da Igwe Ikechukwu Christian, wanda wasu kafafen yada labarai na kasashen waje suka yi hira da su.

Wakilin ya kara da cewa, “Ba za a iya sake su ba har sai gwamnatin Poland ta yanke shawara kan bukatarsu ko kuma ta yanke shawarar janye bukatar.”
Jakadan Najeriya a kasar Poland ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tawagar za ta ci gaba da yin iya kokarinta don ganin an kula da muradun ‘yan Najeriya yadda ya kamata, duk kuwa da cewa an yi musu gargadi sosai kan illar da ke tattare da zama ‘yan ci-rani a kasar ta Poland. .
Idan za a iya tunawa, a watan Maris ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kwashe ‘yan Najeriya da akasari dalibai da suka makale a rikicin Rasha da Ukraine.

Hukumomin cikin gida da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta hadin gwiwa ne suka aiwatar da wannan umarni tare da dawo da ‘yan Najeriya sama da 1,600 zuwa gida.
Duk da haka, wasu daga cikin ‘yan Najeriyar sun zaɓi komawa baya kuma an kulle su a wuraren da ake tsare da su a Poland.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *