Fasinjoji 6 sun kone kurmus a wani mummunan hatsarin bas a jihar Bauchi


Rahotanni daga jihar Bauchi Najeriya na nuni da cewa kimanin fasinjoji 6 na wata motar bas ne suka kone kurmus.

Bas biyu sun kone kurmus a Durum kan hanyar Bauchi zuwa Kano ranar Talata.

Wakilinmu da ke wurin da hatsarin ya faru, ya tattaro cewa hatsarin ya hada da wata mota kirar Sharon Ford da Volkswagen da ke jigilar kaya.

Shaidun gani da ido sun ce an ga fasinjoji kusan shida sun ko-kone a cikin motocin da suka yi karo da juna da misalin karfe 12:15 na dare.

Kakakin hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Rilwan Adamu, ya shaidawa jaridar Guardian cewa, za a samu karin bayani kan hadarin bayan aikin ceto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *