Dakarun sojin saman Israila sun kai hare-hare a zirin Gaza

Dakarun sojin saman Israila sun kai hare-hare a zirin Gaza saoi bayan wani harin roka da Falasdinawan suka kai kan Israila anatsaka da Ibadar Azumi. An ji fashe-fashe da dama a yankin Khan Younis da ke kudancin yankin.

Isra’ila ta ce ta kai harin ne wani wurin kera makamai. Babu dai wani karin haske dangane da asarar rayuka. Tun da farko Isra’ila ta harba makamin roka zirin Gaza, wanda shi ne hari na farko da aka kai tsawon watanni da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published.