Rasuwar Malam Fatima, mahaifiyar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda aka sace sama da shekaru biyu da suka wuce a gidansa da ke unguwar Barnawa a cikin birnin Kaduna.
Rahma Tv ta rahoto cewa ta rasu ne a ranar Talata a Asibitin Sojojin Najeriya na 44 da ke Kaduna inda aka kai ta sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Wani makusancin iyalan na kut-da-kut, Malam Lawal, wanda amini ne ga wan Dadiyata, Usman Idris, ya tabbatar da cewa a halin yanzu, ’ya’yan marigayiyar na kan hanyarsu ta komawa Kaduna, bayan samun labarin rasuwarta.
Dadiyata, malami a Jami’ar Tarayya Dutsen-Ma, ya bace tun lokacin da aka sace shi, kuma ‘yan uwansa suna rayuwa tare da rashin tabbas game da makomarsa.
Allah SWT Ya jikan ta da Rahma.
To Allah ya kyauta