Zulum ya kara albashin ma’aikatan lafiya na jihar Borno.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kara albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai na jihar da kashi 30 cikin 100.

A cewarsa, matakin zai karfafa ayyukan kiwon lafiya a kananan hukumomin jihar guda bakwai da rikicin ya shafa.
Da yake sanar da karin albashin, jiya a Monguno, ya bayyana cewa: “Bayan likitocin, sauran ma’aikatan lafiya kamar ma’aikatan jinya, ungozoma, kwararrun dakin gwaje-gwaje da masu hada magunguna a kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin albashin kashi 20 cikin 100.”

Ya ce karin albashin ne domin zaburar da likitoci da sauran ma’aikatan lafiya wajen kai lafiya mai inganci da araha ga al’ummar Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala/ Balge, Bama da Abadam, a gabar tafkin Chadi.

Ta’addancin da aka shafe shekaru 13 ana yi ya ruguza majalissar, inda Bama ya fi fuskantar hare-hare.

Bayan da babban jami’in kula da lafiya, Dokta Solomon Thiza ya gudanar da zagayen babban asibitin Monguno, gwamnan ya ba da umarnin gina karin rukunin ma’aikata, rijiyar burtsatse da kuma sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana domin samar da ingantaccen aiki.

A watan Janairu ne Zulum ya kara albashin likitocin jihar domin ya yi daidai da tsarin biyan albashin gwamnatin tarayya.

Kazalika, gwamnan ya bayar da umarnin sakin motoci guda biyar domin tallafawa masu sana’ar kifi da ke aiki a tafkin Chadi. Tallafin, in ji shi, an yi shi ne domin a karfafa kamun kifi da rarraba kayayyakin kifi zuwa kasuwannin Arewa maso Gabas.

Da yake bayar da tallafin kamun kifi a karshen mako, a Monguno, ya bayyana cewa: “An dakile ayyukan tattalin arziki a jihar tare da hare-haren Boko Haram a kan ofisoshin sojoji da al’ummomin da ke gabar tafkin Chadi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.