Sojoji sun lalata masana’antar makaman kungiyar ISWAP tare dakashe mayakanta akalla 100, ciki har manyan kwamandojinta atsakiyar watan Ramadan din da muke ciki.


Manyan kwamandojojin kungiyar 10 tare da sauran mayakan sun sheka lahira ne bayan dakarun Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Tafkin Chadi (MNJTF) sun yi musu dirar mikiya sun yi raga-raga da
masana’antar makaman da ke Arina Woje, a yankin Tafkin Chadi.

Kakakin rundunar MNJTF, Kanar Muhammad Dole ya bayyana cewa, Kwamandojin kungiyar da sojoji suka kashe sun hada da Abubakar Dan Buduma, Abubakar Shuwa, Abu Ali da Abu Jubrilla da sauransu.
An kwace muggan makamai, har da makaman atilare, kayan hada abubuwan fashewa, kwalekwale da sauran ababen hawa da sauransu a hannunsu.”

Sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ta ce sojojin sun yi wa mafakar mayakan na ISWAP da ke Zanari da Fedondiya da sauran wurare raga- raga ne ta hanyar amfani da jiragen yaki da kuma dakarun sojin kasa.
An yi nasara kubutar da mutane da dama daga hannunsu, ciki har da mata da kananan yara da suka yi garkuwa da su.

Sauran abubuwan da aka kwace sun hada buhunan hatsi masu tarin yawa, man fetur, miyagun kwayoyi, kakin soji da sauran abubuwa, kuma an lalata su,” inji Kanar Dole.

Ya ce a samamen da sojojin suka kai kan mafakar mayakan na ISWAP a cikin watan Ramadan, a yankin Kimeguna, ta bangaren Jamhuriyar Nijyar, sun kama wasu masu yi wa kungiyar safarar kifi dauke da
buhuna 457 na kifi kuma ana bincikar su.

One Reply to “Sojoji sun lalata masana’antar makaman kungiyar ISWAP tare dakashe mayakanta akalla 100, ciki har manyan kwamandojinta atsakiyar watan Ramadan din da muke ciki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.