Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ya ce yan Najeriya ke da wuƙa da nama wajen kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga


Majiyar mu ta rahoci cewa Wike ya ce abu ɗaya da zai kawo ƙarshen ta’addancin yan bindiga shi ne kawar da jam’iyyar APC daga kan madafun iko tare da maye gurbinta da PDP.

Gwamna Wike ya yi wannan furucin ne a Jos, babban birnin jihar Filato, sa’ilin da ya ke jawabi ga Deleget ɗin PDP na jihar.

Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar jihar su tabbata jam’iyyar PDP ta koma kan madafun iko a 2023 domin ceto jihar daga rugujewa.

Gwamnan ya kuma gaya wa Deleget cewa ya zo ziyara Filato ne somin sanar musu da niyyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa a 2023. Ya jaddada cewa shi ne kaɗai mutumin da ya rage, wanda zai
iya share dukkan dattin da jam’iyyar APC ta kawo wa ƙasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *