Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da gazawa kan harkokin tsaro.

Tsohon Ministan Tsaro wanda kwanan nan ya zama shugaban jam’iyyar (NNPP), ya bayyana hakan ne a
wata tattaunawa da manema labarai a Abuja a jiya Jumma’a.

Kwankwaso ya ce, gwamnati na yaudarar ‘yan Najeriya da cewar suna iya bakin kokarinsu alhali
al’amura na ci gaba da tabarbarewa.

Ya kuma ce zaben 2023 zai shaida juyin juya hali da talakawan Najeriya za suyi na kawar da jam’iyyar
APC mai mulki don samar da sabuwar Najeriya.

One Reply to “Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da gazawa kan harkokin tsaro.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *