Shaharerren Lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil’adama Femi Falana, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saki daukacin fursunonin da aka daure a gidan yari

Shaharerren Lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil’adama Femi Falana, ya yi kira ga shugaban kasar
Muhammadu Buhari da ya saki daukacin fursunonin da aka daure a gidan yari saboda samun su da laifin
sata da wasu laifuka makamanta.

Kiran nashi ya biyo bayan afuwar da Majalisar Koli ta Najeriya wadda ta kunshi tsoffin shugabannin kasa
da tsoffin manyan alkalai da shugaban kasa mai ci da gwamnonin jihohi suka yiwa wasu mutane 159
cikin su harda tosffin gwamnonin jihohin Filato Joshua Chibi Dariye da takwaransa na Taraba Jolly
Nyame.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *