Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin raba hatsi domin a rage radadin tsadar kayan abinci a kasar nan.
Ministan harkarkoin noma da raya karkara, Mohammad Abubakar ne ya kaddamar da wannan shiri a sansanin yan gudun hijira a Karamiji dake garin birnin tarayya Abuja Mohammad Abubakar yace an zabi wannan wuri ne domin wadanda suke gudun hijira suna cikin wadanda suka fi kowa bukatar kayan abinci a wannan lokaci.
Baya ga hatsi, Ministan ya bayyana cewar sauran kayan da ake rabawa sun hadarda ganye da abincin gidan gona da zasu kawo farashi yayi sauki a kasuwa.
Ministan ya kara da cewar ma’aikatar jin kai da bada agajin gaggawa zata raba tan dubu 12, na wadannan kayan abinci ga mabukata.
Inabukata