Fadar shugaban kasa tayi watsi da kiran da dattawan Arewa suka yi na cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi murabus sakamakon kalubalen tsaron da ake fuskanta a Arewa.

Kungiyar dattawan Arewa ta yi wannan kiran ne da yammacin ranar Talata kamar yadda rahotanni suka
fitar Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa daya a ranar Laraba, yace murabus din shugaban kasar ba zai taba zama mafita ga
matsalolin tsaron kasarnan ba.

Kakakin shugaban kasar, ya ce nan bada jimawa ba za’a fara gudanar da sauye-sauye a harkokin tsaron
cikin gida Ya kuma bayyana cewar tuni hukumomin tsaro suka kara kaimi wajen magance yawaitar ayyukan ta’addanci a baya-bayan nan, musamman a jihohin Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta daidai da umarnin shugaban kasa.

A cewarsa, rundunar tsaron kasarnan ta sake daidaituwa tare da sake tsara ayyukan da ake gudanarwa a yankunan da abin ya shafa domin samun sakamako mai kyau. Shugaban kasar ta zargi “masu zagon kasa” da nufin bata gwamnati da nuna ba zata iya magance abubuwan da ke faruwa a kasar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.