Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ɗauki alƙawarin miƙa mulkin Najeriya hannun matasa idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa kuma da matasa zai cika gwamnatinsa.
Ya yi wannan alƙwarin ne a wurin taronsa da shugabannin kungiyoyi sama da 200 dake goyon bayansa da jagororin TeeCom na faɗin ƙasa a Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna jindaɗinsa ganin yadda Matasa suka fito ake damawada su a siyasa, inda ya ce zai horar dasu daga bayakuma ya miƙa musu ragamar tsarin siyasa.
Da za a yi hakan da abun ya yi kyau.
To Amma mun fi son a ce tin daga Shugaban Kasa har zuwa Kansila ya zama tasasa ne akan ragamar mulki .