Ba halinmu bane inji Kwamishanan ‘yan sandan jihar Legas yayin yadda suka kamo jami’in da aka ga yana busa tabar wiwi a bainar jama’a.

An kama wani ASP na ‘yan sanda dake aiki da sashen Shogunle da ke Legas, Babatunde Adebayo, da laifin shan tabar wiwi a bainar jama’a. An dauki Adebayo a kyamara lokacin da yake busa hayakin tabar wiwi yayin da yake cikin wani taro a ranar Lahadi, 10 ga Afrilu.

A sanarwan da ya fitar a yammacin ranar Talata, 12 ga watan Afrilu, kakakin rundunar ‘yan sanda, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa: “Kwamishanan ‘yan sandan jihar Legas, CP Abiodun Alabi, ya bayar da umarnin a fara aiwatar da matakan ladabtar da shi cikin gaggawa da suka dace da matsayinsa.”

Kakakin hedikwatar ‘yan sanda ya tabbatar da kama jami’in Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar sanda, Prince Olumuyiwa Adejobi, shi ma ya tabbatar da kama jami’an a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter.

A sakon da ya wallafa a shafin Twitter, Prince Adejobi ya rubuta cewa: “Mafi rinjaye, halayen rashin da’a suna faruwa ne ta dalilin shan muggan kwayoyi da kuma amfani da su ba daidai ba, har ma wasu ayyuka mara kyau da jami’an tsaro ke yi dalilin shan miyagun kwayoyi ne. Don haka za mu gargade su kafin su yi kuskure ko fiye da haka. Ku yi abin da ya dace a lokacin da ya dace.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *