Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Sanar Da Ranakun Hutun Easter

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a, 15 ga Afrilu da Litinin 18 ga Afrilu, 2022, a matsayin ranakun hutun bukukuwan Eastern 2022.

RAHMA MEDIA ta rawaito cewa babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida Dr. Shuaib Belgore ne ya sanar da hakan a madadin gwamnati, yayin da yake taya mabiya addinin kirista murna.

Belgore ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan biki wajen yi wa kasa addu’ar zaman lafiya.

“Tsaro aikin kowa ne. Don haka ina kira ga ’yan Najeriya da baki mazauna kasarmu da su nuna kishin kasa da kishin al’umma a wannan mawuyacin lokaci na tarihin kasarmu, ta hanyar tallafa wa kokarin dukkanin hukumomin tsaro na samar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyinsu. kadarorin ‘yan kasa,” sanarwar ta ma’aikatar ta kara da cewa.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *